Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da shirya kisan wasu daga cikin mutanen Kudancin Kaduna a lokacin da yake kan mulki.
Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today ranar Alhamis.
Ministan ya ce gwamnatin El-Rufai ta haifar da rarrabuwar kawuna a Kaduna, inda mazauna Kudancin Kaduna suka samu matsala wajen rayuwa a arewacin jihar, haka kuma wasu daga arewacin jihar suka koma kudanci.
Ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani ta yi kokari wajen dawo da haɗin kai da amincewa tsakanin al’ummar jihar.
“Mun san yadda lamarin yake lokacin El-Rufai; abin ya kasance mai guba,” in ji Musa.»
Ya ƙara da cewa, “El-Rufai ya aikata munanan abubuwa da dama a Jihar Kaduna. Ya raba jihar gida biyu. Ta yadda idan kai ɗan kudu ne, ba za ka iya zuwa arewa ka zauna ba. Waɗanda suke daga arewa kuma suna komawa kudu.”
Musa ya ce ko da yake har yanzu ba a kai ga samun cikakken haɗin kai ba, gwamnatin Uba Sani tana yin ƙoƙari wajen haɗa kan al’ummar jihar.
Da yake magana kan yadda mutanen Kudancin Kaduna ke kallon tsohon gwamnan, ministan ya ce har yanzu mutane na fama da radadin kisan da aka samu a yankin a lokacin mulkinsa.
Ya zargi El-Rufai da gangan ya shirya kashe mutanen yankin.
“To, ban san ko rashin farin ciki shi ne kalmar da ta dace ba. Ina ganin idan akwai wani abu da ya fi rashin farin ciki, ba za mu taɓa farin ciki da mutumin da ya shirya kashe mutanenmu da gangan ba,” in ji shi.»
Musa ya kuma yi zargin cewa El-Rufai ya taɓa bayyana a jawabansa cewa ya biya ‘yan bindiga, yana mai cewa tsohon gwamnan bai ɓoye irin waɗannan matakan ba.
Ya ce mutanen Kudancin Kaduna har yanzu suna cikin raɗaɗin tunanin kisan da aka yi a yankin, duk da cewa yanayin tsaro ya samu sauƙi a yanzu.
Ministan ya kuma zargi tsohon gwamnan da tauye wa wasu mazauna Kaduna damar samun abubuwa daban-daban a lokacin mulkinsa, ciki har da mutanen daga yankin da El-Rufai ya fito.
A ƙarshe, Musa ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ƙi goyon bayan ‘yan siyasar da ke amfani da addini, ƙabila ko wasu bambance-bambance wajen raba al’umma.
“Ya kamata mu samu ‘yan siyasar da suke son haɗa kan Najeriya. A wurina, duk mutumin da yake amfani da addini, ƙabila, akida ko wani abu wajen raba jihar, ba zai taɓa zama aboki ba; ba zai taɓa zama mutumin da za mu ɗaga wa kai ba,” in ji Musa.»
Ya ƙara da cewa, “Bai kamata irin waɗannan mutane su kasance cikin gwamnati ba. Duk wanda yake amfani da addini ko ƙabila ko wani abu wajen raba Najeriya, makiyin ƙasa ne.”